Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kaddamar da fara shugabancin Kungiyar Kasashe Masu Karfin Tattalin Arzikin Duniya ta G20 a hukumance bisa taken bukatar dunkulewar duniya da samun daidaito.
Da yake jawabi a yayin kaddamar da fara shugabancin kungiyar ta G20 na Afirka ta Kudu a birnin Cape Town, babban birnin kasar, Ramaphosa ya yi karin haske a kan fara jan ragamar shugabancin kungiyar da Afirka ta Kudu ta yi a ranar 1 ga watan Disamban 2024, wanda ya nuna hawa wani mataki mai tarihi bisa zama kasar Afirka ta farko da za ta jagoranci wannan kungiya ta masu karfin tattalin arzikin duniya.
Ya ce kasar za ta jagoranci kungiyar tare da mayar da hankali musamman ga neman ci gaban tattalin arziki a dunkule, da samun adalci a duniya, da kawar da fatara da yunwa da kuma yaki da sauyin yanayi domin dorewar ci gaban gobe.
A yayin kammala jawabinsa, Ramaphosa ya kuma bayyana cewa, shugabancin Afirka ta Kudu na G20 zai kammala shirya taron koli na shugabanni na kungiyar a watan Nuwamban 2025 a Johannesburg, inda shugabanni na kasashen duniya za su ayyana daukar matakai na hadin gwiwa don tunkarar manyan kalubalen da duniya ke fuskanta.