Africom: Amurka Ta Aike Da Sojoji Zuwa Nigeria Domin Fada Da Ta’addanci

Rundunar sojan Amurka a Afirka ( Africom) ta sanar da cewa, kasar ta aike da sojoji kadan zuwa Nigeria a karon farko tun bayan harin

Rundunar sojan Amurka a Afirka ( Africom) ta sanar da cewa, kasar ta aike da sojoji kadan zuwa Nigeria a karon farko tun bayan harin da ta kai a ranar kirsimeti, a karkashin abinda ta kira aiki tare domin fada da “Da’esh” da Boko Haram.

Kwamandan rundunar ta “Afircom” Dagvin R.M Anderson ne ya sanar da cewa Amurka ta aike da sojoji kadan, zuwa Nigeria.

Wannan shi ne furuci na farko da Amurkan ta yi na cewa, ta aike da sojojinta zuwa kasar Nigeria, tun bayan harin da ta kai a ranar Kirsimeti, bisa zargin da ta yi na cewa, ana kashe Mabiya addinin kirista a cikin kasar.

Tun a baya ne dai kamfanin dillancin labarun Reuters, ya bayyana cewa, jiragen leken asirin kasar ta Amurka suna shawagi a sararin samaniyar Nigeria. Jiragen dai na Amurka suna tasowa ne daga kasar Ghana, sun kuwa fara wannan aikin ne na Leken asiri ne tun a cikin watan Nuwamba.

Kwamandan rundunar sojan Amurkan a nahiyar Afirka ya kuma kara da cewa; An kai sojojin na musamman ne domin kara kaimi a yaki da ayyukan ta’addanci a cikin yammacin nahiyar Afirka.

Shi ma ministan tsaron Nigeria Christopher Musa ya sanar da cewa da akwai wasu sojojin na Amurka da suke aiki a cikin kasar, ba tare da ya yi Karin bayani ba.

 Amurkawan suna cewa aikin rundunar da su ka aike, shi ne tattara bayanan sirri,domin bai wa sojojin Nigeria damar kai hari akan kungiyoyin na ‘yan ta’adda.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments