ADD: Kashi 60% Na Mutanen Da Isra’ila Ta Kashe A Gaza Mata Ne Da Kananan Yara

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa kashi 60% na mutanen da Isra’ila ta kashe a hare-haren da da ta ke kaiwa Gaza mata

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da cewa kashi 60% na mutanen da Isra’ila ta kashe a hare-haren da da ta ke kaiwa Gaza mata ne da kananan yara.

A rahoton shafin arabi 21, kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna cewa mata da kananan yara ne tsakanin kashi 56 zuwa 60 cikin dari ko ma fiye da haka na adadin Falasdinawa da aka kashe a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba.

 An sanar da wannan bayani ne bayan ministan harkokin wajen Isra’ila Yisrael Katz ya sake yi yin dirar mikiya kan Majalisar Dinkin Duniya tare da zarginta da gasgata kididdigar da Hamas ta fitar.

 Katz ya yi ikirarin a cikin shafinsa na “X” cewa ana amfani da bayanan karya na kungiyar Hamas don ci gaba da yin tuhumar aikata  ta’addanci a kan Isra’ila.

 Ma’aikatar lafiya ta Gaza ta sanar da cewa laifuffukan gwamnatin sahyoniyawan sun yi sanadiyar mutuwar mutane 35,173 a zirin Gaza tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Hukumomin da ke da alaka da Majalisar Dinkin Duniya sun ce bayanan ne kadai da abin da aka samu na asarar day akin Isra’ila ya janyo a kan al’ummar yankin zirin Gaza tun daga ranar 7 ga Oktoba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments