Search
Close this search box.

Harin Ta’addanci Ya Yi Ajalin ‘Yan Sanda 15 A Jamhuriyar ta Dagistan

Cibiyar da take fada da ayyukan ta’addanci ta kasar Rasha, ta sanar da cewa a daren jiya Lahadi ne akan kai wani hari na ta’addanci

Cibiyar da take fada da ayyukan ta’addanci ta kasar Rasha, ta sanar da cewa a daren jiya Lahadi ne akan kai wani hari na ta’addanci da yankin Dir-Bint da Mahaj Qal’ah, wanda ya shafi wasu majami’u guda biyu da kuma synagog sannan kuma ofishin ‘yan sanda.

Maharan sun bude wuta akan fararen hula da kuma jami’an tsaro da hakan ya yi sanadiyyar mutuwar fiye da ‘yan sanda 15.

Tuni dai cibiyar da take fada da ayyukan ta’addanci ta kasar Rasha ta bude bincike domin gano hakikanin abinda ya faru.

Tun da fari ma’aikatar cikin gida a jamhuriyar ta Dagistan ta sanar da cewa; An kashe ‘yan sanda 6 sannan kuma aka jikkata wasu 12 sanadiyyar bude musu wuta da aka yi.

Shi kuwa babban muftin jamhuriyar ta Dagistan ya ce adadin wadanda su ka kwanta dama sun kai 9, daga cikinsu da akwai jami’an tsaro 7, haka nan kuma an jikkata wasu mutane 25.

 Wata kafar labarai ta Rasha ta ce; an kama wani jami’in yankin na Dagistan saboda  yadda ‘ya’yansa suke cikin maharan.

.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments