Adadin Falasdinawan  Da Su Ka Yi Shahada A Yammacin Kogin Jordan Sun Kai 534

Cibiyar tattara bayanai ta Falasdinawa ta  ce  a cikin shekarar da ta shude, wato shekara ta 2024 kadai, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada

Cibiyar tattara bayanai ta Falasdinawa ta  ce  a cikin shekarar da ta shude, wato shekara ta 2024 kadai, adadin Falasdinawan da su ka yi shahada a yankin yamma da kogin Jordan sun kai 534, a cikinsu har da kananan  yara 80.

Cibiyar ta kuma kara da cewa; a cikin wannan adadin na shahidai, akwai mata 21 da kuma tsofaffi 23, Har’ila yau hare-hare da sojojin HKI su ka kai a wannan yankin a shekarar da ta gabata, sun shafi gidaje da kuma dukiyar mutanen yankin na yammacin kogin Jordan.

A gefe guda kuma, majiyar asibitin yankin Gaza ta sanar da cewa a cikin sa’oi 24 da su ka gabata, Falasdinawa 66 suka yi shahada, a cikinsu akwai falasdinawa 41 daga arewacin Gaza.

A jiya Asabar ma, ma’aikatar kiwon lafiya ta Falasdinawa a Gaza,  ta bada sanarwan cewa, Sojojin HKI sun yi kisan kiyashi  a wuraren 4  a ranar juma’ar da ta gabata. Inda sanadiyyar hakan an sami shahidai 59 da kuma jikkata wasu 273.

Tun bayana fara yakin tufanul Aksa, a ranar 7 ga watan Oktoba na 2023  zuwa yanzu adadin Falasdinawan da su ka yi shahada sun kai 45,717. Sai kuma yawan wadanda su ka jikkata sun kai dubu 108,856.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments