Search
Close this search box.

Adadin Falasdinawa Da Suka Yi Shahada Sakamakon Hare-Hare ‘Yan Sahayoniyya Sun Kai 41,226

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da aka sun haura zuwa shahidai 41,226 da kuma jikkatan 95,413 Majiyoyin kiwon lafiya

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren wuce gona da iri da aka sun haura zuwa shahidai 41,226 da kuma jikkatan 95,413

Majiyoyin kiwon lafiya na Falasdinu sun sanar a yau Litinin cewa: Adadin wadanda suka yi shahada a Zirin Gaza ya kai Falasdinawa 41,226, wadanda akasarinsu yara ne da mata, yayin da wadanda suka jikkata suka kai 95,413, tun bayan fara kai farmakin sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila kan Falasdinawa a ranar 7 ga watan watan Oktoban bara, baya ga dubban Falasdinawa da abin ya shafa suke karkashin baraguzan gine-gine.

Majiyoyin sun yi nuni da cewa: Sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila sun aiwatar da kisan kiyashi har sau 3 kan iyalan Falasdinawa a Zirin Gaza, ciki har wanda aka yi wa Falasdinawa 20 da suka yi shahada tare da jikkatan wasu 76 wadanda aka kai su asibitoci cikin sa’o’i 24 da suka gabata.

Majiyoyin sun bayyana cewa, har yanzu da yawan daga wadanda abin ya rutsa da su suna karkashin baraguzan gine-gine da kuma kan tituna, kuma motocin daukar marasa lafiya da jami’an tsaron farin kaya sun kasa kai musu dauki saboda killace yankuna da suka yi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments