Shugaban kwarya-kwaryar gwamnatin Falasdinawa Mahmud Abbas Abu Mazin ya ce, babu yadda za a kafa gwamnatin Falasdinu ba tare da an shigar da zirin Gaza a ciki ba.
Mahmud Abbas Abu Mazin ya kara da cewa; Kafa daular Falasdinawa mai babban birnin a Qudus, da kuma komawar ‘yan hijira zuwa Falasdinu, wani abu ne da babu makama zai faru, kuma komai dadewar lokacin, ba za a kauce musu ba.
Haka nan shugaban gwamantin Falasdinun ya ce, suna ci gaba da aiki tukuru, domin samar da sauye-sauye a cikin cibiyoyin gwamnati domin tabbatar da manufar kasar Falasdinu da karawa Falasdinawa karfin gwiwa akan tsayin daka da jurjiya wajen kare hakkokinsu.
Haka nan kuma ya ce, babu yadda za a yi al’ummar Falasdinu ta mika kai ga manufofin yaki, kuma Falasdinawan ba za su fice daga cikin kasarsu ba, don haka za su ci gaba da gwagwarmayarsu ta kare kasa da hakkokinsu na kasa.