Abbas Araqchi ya fadi cewa ya kamata dukkan kungiyoyin kasar Yamen su shiga tattaunawa domin bullo da hanyoyin da za su tunkari makircin makiya na raunanawa da kuma wargaza kasar ta yamen
Araqchi yayi wannan tsokacin ne a wata tattaunawa ta wayar tarho da suka yi da ministan harkokin wajen kasar yamen Abdulwahid Abu ras ta wayar tarho, inda ya jaddada muhummin ci gaba da kare kasar da kuma mutuncinta
Babban jami’in diflomasiya na iran ya jinjinawa alummar yamen game da goyon bayan da suke bawa alummar falasdinu da ake zalunta da kuma tsayin daka da suka yi game da zalunci da gwamnatin isra’ila ke yi
Haka zalika yayi maraba da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin kungiyar Ansarullah dake jagorancin gwamnati da kuma yan aware da saudiya ke goyon baya kan batun musayar fursunoni da ya kunshi mutane 3000.