Search
Close this search box.

A Jiya Talata Ce Aka Cika kwanaki 333 da Fara Yakin Gaza, Adadin Wadanda Aka Kashe Ya Kai Kusan Dubu 41

A jiya talata ce ake cika kwanaki 333 da fara yaki a gaza. Wanda sojojin HKI suka fara don kwato yahudawan da kungiyar Hamas ta

A jiya talata ce ake cika kwanaki 333 da fara yaki a gaza. Wanda sojojin HKI suka fara don kwato yahudawan da kungiyar Hamas ta kama a wasu matsugunan yahudawan kusa da gaza.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa watanni 11 kenan da fara yaki a Gaza, gwamnatin Firai ministan HKI Benyamin natanyahu ta kasa cimma ko da guda daga cikin manufofinta na fara yakin a Gaza.

Kwato yahudawan da suke tsare a hannun Hamas ne gaba-gaba a manufofin Natanyahu firai ministan HKI wanda ya  fara yakin, amma gwamnatinsa ta kasa samun haka sai gawakinsu daya bayan daya cikin fursinonin.

Ya zuwa jiya Talata 3-9-2024, watanni 11 da fara yaki a gaza, sojojin yahudawan sun kasha  Falasdinwa akalla 40,700 sannan wasu 91 sun ji raunuka.

Sai dai duk tare da kisan kiyashin da sojojin yahudawan sukewa fararen hula a Gaza, yahudawan sun kasa cimma ko da guda daga cikin manufofinsu na fara yakin.

Yahudawan HKI dai suna samun goyon bayan Amurka da kasashen yamma. Mafi yawan makamansu na fitowa ne daga kasar a Amurka. Sannan tana bada dukkan kariyar da HKI take bukata a fagen kasa da kasa musamman a MDD.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments