Search
Close this search box.

A Gobe Litinin Ne Ake Saran Za’a Fara Yajin Aiki A Duk Fadin Tarayyar Najeriya Saboda Matsalolin Daban Daban

Kungiyoyin kwadago a tarayyar Najeriya sun sha alwashin shiga yajin aiki sai baba ta gani saboda gabatar da korafe korafensu dangan da matsin rayuwa wadanda

Kungiyoyin kwadago a tarayyar Najeriya sun sha alwashin shiga yajin aiki sai baba ta gani saboda gabatar da korafe korafensu dangan da matsin rayuwa wadanda suka hada da karancin albashi, rashin wutan lantarki, rashin makamashi matsalolin tsaro da ababen hawa da sauransu.

A cikin wani bayani wanda manya manyan kungiyoyin kwadago a kasar wato NLC da kuma TUC suka fitar sun bukai dukkan ma’aikata su yi biyayya ga umurnin shuwagabannin kwadago don tabb atar da cewa yajin aiki ya game dukkan kasar don samun biyan bukata.

Labarin yan kara da cewa yajin aikin zai shafi dukkan ma’aikatun gwamnatin wadanda suka hada da makarantu, asbitoci, tashoshin jiragen ruwa da na sama. Don haka yajin aikin zai haddasa wahalhalu a bangarorin tafiye tafiye da kuma da kuma karancin man fetur.

Kungiyoyin sun bayyana cewa nasarar yajin aikin ya danganci irin hadin kan da mutane suka bayar na shiga yajin aikin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Inline Feedbacks
View all comments