Malasiya: Babu Bukatar Kasashen Yamma Su Koyawa Musulmi Menene Kare Hakkin Bil’adama Ko Demokradiyya

Farai ministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim ya bayyana cewa kasashen musulmi basa bukatar kasashen yamma su koya masu me ake nufi da demokradiyya ko kare

Farai ministan kasar Malasiya Anwar Ibrahim ya bayyana cewa kasashen musulmi basa bukatar kasashen yamma su koya masu me ake nufi da demokradiyya ko kare hakkin bil’adama.

Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Anwar Ibrahim yana fadar haka a bikin bude wani masallaci a birnin Kwalalampo na kasar, ya kuma bayyana yadda kasashen yamma suke son karkata labaran gaskiyan abinda yake faruwa a Gaza, ta kafafen yada labaransu na kasa da kasa.  

Firai ministan ya kara da cewa ba’a fara yakin Gaza a ranar 7 ga watan Octoban shekara ta 2023 ba, sai dai an fara yakin ne tun shekara 1948 a lokacin turawan ingila suka kafa HKI a kan kasar Falasdinu da suka mamaye bayan yakin duniya na daya.

Kafin haka dai gwamnatin kasar Malasiya ta haramtawa kamfanonin HKI shigowa kasar don harkokin kasuwanci ko wani abu mai kama da haka. Sannan a wani taron da shuwagabannin kasashen Malasiya da kuma Tsibirin Burunai suka gudanar sun nuna damuwarsu kan yadda al-amura suke kara tabarbarewa a gabas ta tsakiya da kuma yadda yakin Gaza yake kara fadada a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments