Ministan harkokin waje na HKI “Yisrail Kats” ya wallafa hoton shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan a shafin “X” sannan ya kuma rubuta cewa: Yana yi wa Isra’ila baraza, don haka mutuwa ce a gabansa.”
Shi dai shugaban kasar Turkiya yana Magana ne akan abubuwan da suke faruwa a Falasdinu, inda ya bayyana cewa; Wajibi ne kasar Turkiya ta zama mai karfi, saboda kada Isra’ila ta yi abinda take yi a Falasdinu.
Bugu da kari shugaban kasar ta Turkiya ya bayyana cewa; Turkiya za ta iya shiga cikin Isra’ila, kamar yadda ta shiga Libya da kuma yankin “Qareh-Bah’ na Azerbaijan.”
Ma’aikatar harkokin wajen kasar Turkiya ta fitar da bayanin mayar da martani da aciki ta bayyana cewa; Wadanda su ke yi wa Falasdinawa kisan kiyashi su kwana da sanin cewa ba su isa su kawo karshensu ba.
Sanarwar ta kuma kara da cewa; Kamar yadda kisan kiyashin Hitler ya zo karshe, to kiashin kiyashin na Benjamine Netenyahu yake yi, shi ma zai zo karshe.