Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump Ya Gargadi Kungiyar Hamas Kan Amurkawa Da Ta Kama

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kungiyar Hamas da cewa zata dandana kudarta idan ba ta saki Amurkawan da take tsare da su ba

Tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya gargadi kungiyar Hamas da cewa zata dandana kudarta idan ba ta saki Amurkawan da take tsare da su ba

Tsohon shugaban kasar Amurka Donald Trump ya gargadi kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hamas tare da mata barazanar cewa za ta biya babban farashi, idan har ba ta hanzarta sakin fursunoni Amurkawa da ta yi garkuwa tare da ci gaba da tsare su a Zirin Gaza ba.

A jawabin da Trump ya gabatar a gaban dubban magoya bayansa da suka taru domin halartar babban taron jam’iyyar Republican a Milwaukee, Wisconsin ya yi furuci da cewa: Suna son wadanda aka yi garkuwa da su, su dawo gida, kuma ya fi zama alheri ga Hamas ta sako su don su dawo ga iyalansu kafin ya hau mulki, idan ba haka ba, Hamas za ta biya farashi mai yawa, a cewarsa.

Trump ya kara da cewa; Zai kawo karshen yakin da ake yi a Zirin Gaza, wanda ake ci gaba da gwabzawa tun a watan Oktoban shekarar da ta gabata, inda ya yi alkawarin kwato fursunonin Amurka kafin rantsar da shi idan ya lashe zaben shiga fadar White House.

Tsohon shugaban na Amurka ya sanar da amincewarsa da matakin jam’iyyar Republican na tsayar da shi dan takara a zaben shugaban kasa da aka shirya gudanarwa a watan Nuwamba mai zuwa, inda ya yi alkawarin warware duk wasu rikice-rikicen da gwamnati mai ci ta haifar da su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments