MDD, ta bayyana cewa ana bukatar samar da cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin domin samuwar kwararar kayan agajiu zuwa Gaza.
Domin agaji ya kwarara zuwa Gaza, akwai bukatar a samar da ‘cikakkiyar tsagaita wuta ta dindindin’ Kamar yadda, Sigrid Kaag, jami’ar kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya a Gaza, ta bayyana wa kwamitin sulhu MDD, kan halin da ake ciki na baya-bayan nan a yankin.
Jami’ar ta ci gaba da cewa ba a kai isashen agajin da ake bukata ya shioga shiga a Gaza ba.
Ms Kaag ta kuma mai da hankali kan bukatar kungiyoyin Majalisar Dinkin Duniya su sami karin “hanyoyi daban-daban da ke shigowa cikin Gaza” kuma ta ce tana tattaunawa da jami’an Isra’ila don yiwuwar sake bude babbar hanyar Rafah, a wani mataki na farfado da yankin.