Qasim Al-Araji mai bawa shugaban gwamnatin kasar Iraki shawara kan al-amuran tsaro ya gana da shugaban majalisar koli ta tsaron kasar Iran Janar Mohsen Rizaei a nan Tehran.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Araji na cewa bangarorin biyu sun bukaci a aiwatar da yarjeniyoyin da kasashen biyu suka rattabawa hannu a baya dangane da harkokin tsaro tsakanin kasashen biyu. Har’ila yau sun bukaci a kara karfafa harkokin tsaro a kan iyakokin kasashe biyu.
Janar Rizaei ya kara da cewa kasar Iraki mai karfi zata taimaka wajen tabbatar da harkokin tsaro a yankin wanda zai kasnace maslaha ga kasashen yanking aba daya.
Shugaban majalisar kolin ta tsaron kasar Iran ya kara da cewa, akwai bukatar kasashen biyu su kara bunkasa harkokin kasuwanci tsakaninsu ba tare da shishigin wata kasa daga waje ba.
Sai kuam Al-Araji wanda ya sha alwashin ganin an aiwatar da dukka kuma cikekken yarjeniyoyin da aka cimma tsakanin kasashen biyu. Daga ciki ba zata amince a yi amfani da sararin samaniyar kasar don kaiwa kasar Iran hare hare kamar yanda Amurka da Isra’ila suka yi a ba ya ba. Ko wata kasa daga cikin kasashe makobta ba.