Wani masanin tattalin arziki ɗan Amurka ya musanta ikirarin jaridar New York Times game da madatsun ruwa na Iran
Masanin tattalin arziki na Amurka kuma mai ba da shawara kan tantance haɗari, Brett Erickson, ya yi kira ga jaridar New York Times da ta janye wani labarin da ta buga a ranar 16 ga Nuwamba, mai taken “Yaƙi Zai Iya Zama Amsar Tsohon Matsala na Madatsun Ruwa na Iran da aka Gina Ba Tare da Wani Dalili Ba,” sannan ta fitar da sanarwa da ke fayyace “Kai hari kan kayayyakin more rayuwa na ruwa a Iran domin ya saba wa doka.”
A wani rubutu da ya wallafa a dandalin X, Erickson ya zargi ‘yan jarida Erika Solomon da Sanam Mahoozi—wadanda su ne suka rubuta makalar—da yunkurin rinjayar ra’ayin jama’a domin su amince a sanya madatsun ruwa da kayayyakin more rayuwa na ruwa na kasar Iran a matsayin “kayayyakin more rayuwa masu amfani iri biyu” (dual-use infrastructure). A cewarsa, hakan na iya bai wa Amurka hujjar kai hari kan irin wadannan wurare, bisa tanadin dokokin kasa da kasa.
Ya lura cewa Mahozzi ya rubuta a kan dandalin X cewa: Bincike na tsawon watanni bai sami wata shaida mai gamsarwa ba cewa wasu ayyukan ruwa na Iran sun ba da gudummawa ga gina sojoji, ya ƙara da cewa lamarin ya haifar da “tambayoyi da suka cancanci bincike.”