Limamin da ya jagoranci sallar Jumma’a a nan Tehran ya bayyana cewa nasara a kan makiya yana cikin biyayya ga jagoran juyin juya halin musulunci.
Jaridar Tasnim na kasar Iran ya nakalto Sheikh Muhammad Jawad Ali Akbari, yana fadar haka a cikin khudubobinsa na sallar Jumma’a a yau a nan tehran, ya kuma bayyana haka a lokacinda yake magana dangane ayayin suratul Fatahi, da kuma gabatar da littafin da aka rubuta dangane da nasarori, bisa mahangar Imam Shahida (q).
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto Limamin yana cewa, mutanen kasar Iran sun rabauta ta samun shuwagabannin kamar Imam Khumaini (a) da kuma Imam Shahid (R). Yace wannan littafin an rubuta shi ne daga khudubar da Imam Shahida (R) ya gabatar shekaru 37 da suka gabata, yana kuma danganta maganarsa da ayoyin alkur’ani mai girma.
Ya ce Imam Shahid (R) ya sifanta mutanen Iran amatsayin mutane masu basira masu fahintar yadda al-amura suke tafiya a duniya, kuma sun gajiyar da makiyansu da wadannan halaye. Sun nunawa duniya cewa su yentattu ne, basa jin tsaron kawo daga cikin manya manyan kasashen duniya.