Babban kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci (IRGC) ya bayyana cewa wadanda suka aikata laifuka a Iran basu da wurin buyewa da hutu a nan duniya.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Manjo Janar Ahmad Wahidi yana fadar haka a yau Jumma’a a bikin rufe wani taro a nan Tehran. Ya Kuma Kara da cewa, yakin da Amurka da kuma haramtacciyar kasar Israela suka dorawa kasar Iran tun watan Fabrayrun da ya gabata, yaki ne wanda suka kasa cimma manufofinsu a cikinsa.
Janar Wahidi ya ce “Masu talakalar yakin ba za su tsira ba, masu kissan mutanen musamman yan makaranta a garin Minab ba zasu zauna lafiya ba, bayan sun aikata wanya manyan laifuka. Haka ma wadanda suka kashe jagoran juyin juya halin musulunci ba zasu taba samun wurin boyewa a nan duniya ba.
Janar Wahidi ya ce “Dole ne su ji tsoro su yi karkarwa su ji tsoron laifukan da suka aikata, … saboda Iraniyawa suka da hakkin su dauki fansa a kan wadanda suka aikata wadannan manya manyan laifuka.”
A wani bangare a maganarsa, babban kwamandan IRGC y ace “Mun wace bangare mai yawa na yakin, amma kuma akwai wani bangare mai yawa da ya rage mana”. Ya ce” Abinda muka aikata ya zuwa yanzu, ya sanya makiya jin cewa an sami nasara a kansu, an wulakanta su, sun zama mabukata, sun rikice. A farkon yakin sun yiwa kasashen larabawa na yankin Tekun farisa, alkawalin zasu gama da Iran a cikin sa’o’ii 72, da hakan bai yu ba sai suka ce makonni biyu. Amma shi ma wuce ba tare da samun nasara ba.”
Yace “suna son chanja, tsarin JMI amma sais u suka sauya kansu”. Sun kuma kawo manya manyan makamai don su tsorata mutanen kasar amma sun kasa kawosu wadannan manya manyan makamai kusa da Iran.
Daga karshe Janar Wahidi y ace “A halin yanzu saojojin ruwa na IRGC NAVY” suna iko da ruwayen tekunan yankin har zuwa kilomita 500 daga daga bakin ruwa.