Mokhber : Dakarun Iran Na Cikin Shiri Fiye Da Ko Wane Lokaci

Wannan gargadin ya zo ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa Iran na iya fuskantar sabon hari daga Amurka da Isra'ila.

Wani mai ba Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran shawara ya bayyana cewa tsarin tsaron Iran yana cikin wani mataki na shiri fiye da ko wane lokaci, kuma kasar ba za ta yi wasa ba da daukar fansarta ga hare-hare kan kadarorin masu kai mata hari a yankin ba.

A wani sako da ya wallafa a shafinsa na X yau Lahadi, Mohammad Mokhber ya ce Iran tana canza dabarunta na soja da hana hare-hare “cikin sauri,” domin ba ta damar kai hari kan wurare da ke nesa da yankin Yammacin Asiya, a matsayin martani ga duk wani sabon hari da ka iya faruwa kan ta.

Wannan gargadin ya zo ne a daidai lokacin da ake fargabar cewa Iran na iya fuskantar sabon hari daga Amurka da Isra’ila.

Iran ta nuna cewa za ta mayar da martani mai tsauri ga duk wani sabon hari, inda jami’an soja da na tsaro suka yi gargadin cewa girma da karfin martanin da za ta mayar a wannan karon zai fi na baya nesa ba kusa ba.

A ranar Asabar, Jagoran Juyin Juya Halin Musulunci na Iran, Ayatollah Khamenei ya umurci manyan hafsoshin sojan Iran da su shirya domin kai martani mai sauri da karfi ga duk wata barazana, “ba tare da la’akari da iyakoki ko wuri ba.”

A daya bangaren kuma, masu shiga tsakani daga kasashen yankin na kokarin neman mafita ta hanyar diflomasiyya ga takun-sakar da ke tsakanin Iran da Amurka, yanayin da ya haifar da rudani a harkokin samar da makamashi da kayayyaki a duniya.

Iran ta bayyana cewa a shirye take ta karbi irin wannan mafita ta diflomasiyya, muddin Amurka ta amince da sharudanta na kawo karshen hare-haren har abada, tare da dage takunkumai da killacewar da aka wa tashohin jiragen ruwanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted