Faransa : Dalibai Sun Sha Alwashin Ci Gaba Da Toshe Makarantu

Bayyanai na ranar 31 ga watan Oktoba sun nuna cewa mutane ​​565 aka cafke a yayin zanga zangar.

Kungiyoyin daliban makarantun sakandare da na jami’a a faransa sun sha alwashin ci gaba da toshe makarantu a mako duba da matakan da gwamnatin kasar ta dauka a yayin zanga zangar da aka gudanar a jiya Asabar.

Mai magana da yawun kungiyar daliban, Sabrine Kharbach, ta yi kira a ranar Asabar da a toshe makarantun sakandare da jami’o’i a ranar Talata da Alhamis mai zuwa, don mayar da martani ga matakin Paris.

A jiya ne aka gudanar da zanga zanga kan tsadar rayuwa a Asabar ta uku a jere.

Bayyanai na ranar 31 ga watan Oktoba sun nuna cewa mutane ​​565 aka cafke a yayin zanga zangar.

A cewar hukumomi, mutane 320,000 suka shiga zanga zangar.

An sake yin kone kone da shafe shafe da kuma artabu tsakanin ‘yan sanda da masu zanga zangar.

Babban jami’in ‘yan sanda na Faransa ya yi Allah wadai da “tashin hankalin da ya ce ba a taba gani ba”

Faransa ta jibge ‘yan sanda da jami’an tsaro kimanin 70,000 a fadin kasar gabanin sabuwar zanga zangar da aka tsara gudanarwa jiya Asabar.

Wannan gangamin ya zo ne bayan zanga-zangar da aka gudanar Asabar biyu a jere, a ranakun 17 da 24 ga Oktoba.

Tun daga tsakiyar watan Satumba ne, aka fara gangamin da ya rikide zuwa zanga-zanga, wanda daliban makarantar sakandare suka jagoranta saboda matsalolin da suka ce sun dabaibaiye sha’anin daukar karatunsu, wanda kuma ya samu karbuwa a duk fadin kasar.

Zanga-zangar wani bangare ne na boren da ya barke saboda tsadar rayuwa, tabarbarewar yanayin ilimi, hauhawar farashin mai, da kuma yadda ‘yan sanda ke murkushe masu zanga-zangar lumana.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted