Gwamnatin kasar Iran ta sanya hukumar leken asiri ta kasar Burtania wacce aka fi sani da M16 a matsayin hukuma mai husumi da ita, sannan sojojin ruwa da kuma sama na kasar Burtania wato ‘ the Royal Navy da Royal Air Force’ a matsayin kungiyoyin yan ta’adda a wajenta.
Kamfanin dillancin labaran IRNA na kasar Iran ya nakalto ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran na fadar haka a safiyar yau Lahadi, ta kuma kara da cewa, Iran ta dauki wannan matakin ne saboda maida martani ga gwamnatin kasar Burtania wacce ta sanya dakarun kare juyin juya halin musulunci na kasar Iran wato IRGC a matsayin kungiyar yan ta’adda kuma wacce take barazana ga kasar Burtania a farkon wannan shekarar.
Sanarwan ta kara da cewa majalisar koli ta tsaron kasar Iran ce ta zauna ta kuma tabbatar da cewa zata dauki duk matakan da suka dace kan wadanda hukumomin tsaro na kasar Burtania dai dai yanda dokokin kasar Iran suka tanadar.
Sanarwan ta kara da cewa, matakin da gwamnatin Burtania ta dauka a ranar 13 ga watan Yulin shekara ta 2026 kan IRGC tun farko ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Banda haka yace, gwamnatin Burtania tana da hannu dumu dumu a tallafawa HKI a yakin da take fafatawa da ita a nan Iran da kuma kasar Falasdinu da aka mamaye.