Shugaban Iran ya taya takwaransa na Iraki murna

Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya taya takwaransa na Iraki Nizar Amid, murna akan zabin da akayi masa a matsayin sabon shugaban kasar.
Shugaban Iran ya taya takwaransa na Iraki murna

Shugaban kasar Iran, Massoud Pezeshkian, ya taya takwaransa na Iraki Nizar Amid, murna akan zabin da akayi masa a matsayin sabon shugaban kasar.

A cikin sakon na san a taya murya Pezeshkian, ya tabo batutuwan da suka shafi tarihi, al’adu da kuma addini da ya suka hada kasashen biyu Iran da Iraki kasashe biyu masu tasiri a yankin da kuma kasashen musulmi.

Ya kuma yi fatan zuwan Amid a shugabancin zai kara karfafa huldar siyasa, hadin guiwa tsakanin Tehran da Bagadaza a dukkan bangarori fiye da ko wane lokaci.

Haka zalika shugaban kasar ta Iran, ya yi fatan zabin da akayi wa Amid a matsayin shugaban kasar Iraki, zai sanya kara hadin guiwa tsakanin gwamnatocin kasashen biyu ta fuskar tsaro da tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin.

Kafin nada shi a matsayin shugaban Iraki, Amidi, ya kasance ministan kula da mahali a gwamnatin firaminista Mohammed Shia al-Sudani na tsawon shekaru biyu kafin ya yi murabus daga mukamin a shekarar 2024.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted