Gwamnatin Iran Ta Jinjina Wa Al’ummar Kasar Kan Fitowarsu Domin Nuna Goyon Baya Ga Tsarin Musulunci

Gwamnatin Iran ta bayyana cewa, juyin juya halin muslunci a kasar yana ci gaba da kasacewa ne bisa goyon bayan al’ummar kasar.

Gwamnati ta jinjina wa al’ummar Iran kan yadda suke fitowa kullum rana kwansu da kwarkwatarsu suna yin Allawadai da harin da ake kaddamar a kan kasarsu.

Ta ce wannan goyon bayan tare da tsayin dakan al’umma da kuma turjiya ta dakaru da ke fagen daga su ne babban sirrin wanzuwar juyin.

Ta ci gaba da cewa, makiyan kasar Iran sun jahilci al’ummar wannan kasa, domin kuwa suna tunanin cewa ta hanyar kasha jagorori kasar za ta rushe, amma abin da ya faru akasin haka ne.

Sannan kuma ya jadda wajabcin ajiye sabani na siyasa ko fahimta a gefe guda, tare da fifita maslahar kasa a kowane lokaci, wanda kuma shi ne zai kara tabbatar da hadin kan al’ummar kasar domin tunkarar kalubale.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted