Babbar Jami’ar MDD ami bincike ta bayyana cewa, abin day a faru a Gaza kisan kare dangi ne.
A cikin rahoton nata, babbar jami’ar ta MDD ta bayyana cewa, bisa bincike da aka gudanara dukaknin bangarori, an gano muhimman abubuwa ad suka shafi kisan ganganci a kan kanan yara da mata da tsoffi da sauran fararen hula.
Ta ce a bisa dokokin kasa da kasa wannan aikin yana matsayin laifin yaki, kuma dole ne a dauki mataki na shari’a a kansa.
Rahoton na MDD ya hada bangarori daban-daban na kasa da kasa da kuam kungiyoyi masu zaman kansu, wadanda dukkansu sun sun fitar da bayanai kan laifukan yaki da Isra’ila ta aikata a Gaza.
Duk da cewa tuni an riga an gurfanar da Isra’ila a gaban kotun duniya kuma an bayar da sammacin kame Netanyahu da tsohon ministan yakin Isra’ila, amma har inda yau take tana ci gaba da yin kisan gilla a kan al’ummar gaza.