Sakon Ayatollah Sayyid Mujtaba Khamenei Na Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyya 1405

Ya mai sauya zukanta da maganai, ya wanda yake tafiyar da dare da rana, ya mai sauya yanayi da halayya, ka sauya halayenmu zuwa mafifita.
Sakon Ayatollah Sayyid Mujtaba Khamenei Na Sabuwar Shekarar Hijira Shamsiyya 1405

Da sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Kai

Ya mai sauya zukanta da maganai, ya wanda yake tafiyar da dare da rana, ya mai sauya yanayi da halayya, ka sauya halayenmu zuwa mafifita.

Ina mika sakon taya murna ga daidaikun mutanen Iran na bukuuwan idi biyu na addini, karamar salla, da kuma na tsohuwar al’ada ta kasa, na sabuwar shekara -Noruz, da a bana su ka zo a hade a lokaci daya. Ina mika murnar bikin karamar salla musamman ga dukkanin al’ummar musulmin duniya.

Haka nan kuma ya zama wajibi in bijiro da sakon taya murna saboda nasarori masu yawa da sojojin musulunci suke samu, ga dukkanin iyalai da dangin shahaidan masu girman matsayi na kallafaffen yaki na biyu, da yunkurin juyin Mulki na watan Dey ( watan 10 na hijira shamshiyya) da kallafaffen yaki na uku, da kuma shahidan jami’an tsaro da masu tsaron kan iyakokin kasa da jami’an tsaro na farin kaya. Ina mika sakon ta’aziyya da juyayi a gare su.

Danagne Da Shiga Sabuwar Shekarar Hijira Shamshiyya 1405 Ina Da Wasu Abubuwan Da Zan Bijiro Da Su A Kasa Da farko, zan yi takaitacciyar bitar abubuwan da su ka faro a cikin shekarar da ta gabata. A cikin shekarar da ta wuce, al’ummarmu ta fuskanci yake-yake guda uku, na soja da na tsaro. Yaki na farko, wanda ya faru a cikin watan Yuni wanda ‘yan sahayoniya bisa taimakon musamman daga Amurka su ka shelanta ana tsakiyar tattaunawa. Hari ne na yankan baya,wanda a sanadiyyarsa manyan kwamandoji da masana na kasa da kuma wasu mutanen da sun kai 1000 su ka yi shahada. Makiya sun yi kuskuren lissafi, sun tsammaci cewa bayan kwana daya ko biyu, za su iya kifar da tsarin musulunci. Sai dai saboda basirar al’umma da sanin ya-kamata mara tamka na sojojin musulunci da sadaukar da kai mai yawa da aka yi, ba a je ko’ina ba, -makiyan-su ka zama abin tausayi, su ka sauko daga kan doguwar bishiyar da su ka hau ta hanyar kamun kafa da shiga Tsakani.

Yaki na biyu, shi ne yunkurin juyin Mulki na watan Dey ( watan 10 na shekarar hijira shamshiyya), Amurka da ‘yan sahayoniya sun tsammaci cewa saboda matsin lamba na tattalin arziki da -su ne-su ka damfara musu, za su yi aikin da makiyan suke so, so ka yi amfani da ‘yan korensu wajen aikata ta’asa mai yawa. Su ka kuma zama sanadiyyar shahadar ‘yan kasarmu da yawansu ya fi na wadanda su ka yi shahada a yakin da ya gabace shi, da kuma haddasa asara mai yawa-ta dukiya.

Yaki na uku kuwa, shi ne wanda muke ciikinsa a yanzu. A ranarsa ta farko, uba ga al’umma mai tausayawa a gare ta, jagoran juyin musulunci, Allah ya daukaka matsayinsa, ya shiga cikin shahidai da siddikai a cikin shaukin haduwa da Allah. Mu kuwa mun yi bankwana da shi a cikin zubar hawaye da bakin ciki.

Haka nan kuma bayan wannan ranar, mu ka ci karo da shahadar kananan yara ‘yan makarantar “Shajaratul-Dayyibah” a garin Minab, sai kuma mu ka ci karo da jaruman shahidan jirgin ruwa na Dana, da kwamandoji da mayaka shahidai na dakrun kare juyin musulunci ( IRGC). Sai shahidan sojoji da ‘yansanda da dakarun sa kai ( Basij) da jami’an tsaro masu farin kaya da masu tsaron kan iyakoki da sauran daidaikun mutane ‘yan kasa da su ka yi shahada, daga kan kananan yara zuwa manya, duk sun shiga cikin runduna ta haske da su ka gitta ta gaban idanunmu. Duk mun yi bankwana da su a cikin bakin ciki. Bayan da makiya su ka yanke kauna akan cewa wasu mutane za su fito domin su yi musu aiki, da kuma yin mafarkin tsaye akan cewa idan jagoran juyi da kwamandojin sojoji masu tasiri su ka yi shahada, to ku al’ummar kasa za ku fada cikin razana da tsoro, don haka za ku koma gefe, sai ya zama sun sami damar shimfida ikonsu akan Iran, su kuma karkatsa ta.

To amma sai ya zamana a cikin wannan watan na azumin Ramadan, kun hada shi da aikin jihadi, da kasantuwa a cikin filin dagar kare kasa da yin tsayin daka a cikinsa a cikin unguwannida masallatai. Wannan abinda ku ka yi ya gigita abokan gaba, ta yadda su ka rika yin maganganu masu cin karo da juna da sambatu da hakan yake nuni da karancin sanayyarsu da al’ummar Iran.

Gabanin wannan lokacin, kun murkushe juyin mulkin ranar 22 ga watan Dey da ranar 22 ga watan Bahman. Wani karo ne da ku ka tabbatar da yadda ku ka raba hannun riga da masu girman kai na duniya. Kun nuna rashin gajiyawa, a wannan lokacin da kuma a ranar 22 ga watan Isfand da ita ce ranar Qudus, da ku ka rubanya kwazo. Kun sake kwankwasar kan makiya ku ka tabbatar masa da cewa ba da makamai masu linzami da jirage marasa matuki ne kadai kuke yaki da shi ba, fagen dakar Iran ya tsallake duk wani karamin tunaninsa.

Zan yi amfani da wannan damar, domin in yi godiya ga daidaikunku mutanen-Iran-masu daraja, saboda wannan kumajin da su ka nuna; haka nan godiya ga shugaban kasa da yake gwarzo, mai gaskiya wanda yake mutumin mutane, da kuma sauran jami’an gwamnati da su ka halarci wannan gangami ba tare da wani banbanci da sauran mutane ba.

Wannan wani aiki ne mai girman matsayi akan kansa, wanda kuma zai kara bunkasa alaka a tsakanin al’umma da mahukunta.

A halin da ake ciki, an sami Karin dankon zumunci na alaka a tsakaninku da kuma ‘yan kasa ta fuskoki da dama da su ka hada, addini, tunani, al’ada da siyasa. Su kuwa makiya sun kara cin kasa. Ya kamata a dauki wannan a matsayin wata ni’ima ta musamman daga Ubangiji madaukakin sarki,da ya zama wajibi a yi masa godiya da harshe da kuma aiki.

Daga cikin abubuwan da bai kamata a yi saku-saku da sub a, da akwai yin godiya a duk inda aka sami wata ni’ima, kuma gwargwadon yadda ake yi godiyar akan kara samun tsayin daka da kuma daukaka. Haka nan samun kulawa ta musamman daga Allah wacce wanda ya yi wannan godiyar zai samu.

Yin godiya a aikace shi ne mu dauki wannan Babbar ni’imar daga Allah a matsayin ni’ima daga gare shi madaukakin sarki, kuma mu yi aiki da ita iya karfi. Yin hakan zai sake tabbatar da hadin kai mai karfi, ya kuma kaskantar da makiya.

Wannan ce bitar muhimman abubuwan da su ka faru a 1404

A wannan sabuwar shekarar ta 1405 da mu ka shiga, muna fuskantar wasu batutuwa. Na farkonsu shi ne, muna yin bankwana da watan azumin Ramadan na 1447 da mu ka kasance baki a cikins yana yin bankwana da mu.Wata ne wanda a cikinsa da akwai daren “Lailatul-Qadari” da zukatanku su ka nutse wajen yin addu’a ga Allah madaukakin sarki da rokonsa, wanda kuma rahamarsa ta lullube ku. A cikin wannan daren kun roki Allah da yin tawassuli da jagoranmu Imam Zaman Allah ya gaggauta bayyanarsa akan samun nasara da sauran ni’imomi daga gare shi. Kuma da yardar Allah, Allah zai karba muku addu’oinku da abubuwan da ku ka roka, ko ma ya ba ku mafificin abinda ku ka roka.

A cikin yanayi irin wannan na bankwana, gwargwadon yadda ake da sanayya mai tsawo da wanda ake rabuwa da shi, zuciya take kasantuwa cikin damuwa a bakin ciki mai zurfi. Jaririn watan Shawwal mai albarka wanda yake matso mu, muke kuma tattare da tsoro da fata a wurin Allah madaukakin sarki,da zai zama shi ne goron sallar da za mu karba. Bayan yadda ku ka kasance a cikin fagage dare da rana kuna aiki da nauyin da ya rataya a wuyanku, da fitowarku mai cike da kumaji a ranar Kudus ta duniya, ina fatan Allah madaukakin sarki ya yi mana baiwa bakidaya da karamcinsa, ya ba mu hakuri, ya yi mana afuwa da ludufinsa.

Ina kuma mai fata na musamman cewa ba da jimawaba, za mu sami busharar bayyanar babban waliyin Allah, ma’abocin zamani, da hakan zai cika zukatanmu da farin ciki, ya kuma cika al’ummar duniya da albarka,bisa baiwarsa da kaaramcinsa.

Abin da ke a  gabanmu yanzu shi ne Idin tarihi na Noruz. Idi wanda yake tattare da abubuwa na kyawun dabi’a sannan kuma a daya bangaren yana tattare abubuwa masu ma’ana ta fuskar ruhi.

Ga sauran mutane wannan shi ne lokacin da ake bukin sabuwar shekara ba tare da shahidin  jagoranmu da sauran shahidai masu madaukakin matsayi ba. Musamman ma ga iyalai wadanda suka rasa danginsu.

Ni kai na a matsayin dan kasa kamar kowa, ina zaton cewa ina daga cikin masu makoki saboda wasu daga cikinmakusanta nawa da suka yi shahada, amma kuma a lokaci guda muna cikin farin cikin cewa sabbin anguna da sabbin surukai sun shiga cikin rayuwa ta ni’ima, da yardar Allah addu’ar shihidin jagoranmu da sauran manyan shahidai na wannan yaki za ta riske su.
Ina  yin kira ga sauran jama’a a wannan lokaci da ake ziyara a kula da yanayin da iyalan shahidai suke ciki.
Idan har zai yiwu tare da hadin gwiwa a tsakanin mutane a yankuna, tarukan wannan shekara su  zama taruka ne na girmama shahidan wannan yankin.

Duk da cewa gwamnati ta yanke cewa, juyayin shahadar jagoranmu yana nan a kan bakansa, kuma kiyaye hakan wani babban bangare ne na matsayin juyi da kuma kasa.

Bayan wadannan kalmomi akwai wasu abubuwan da nake son in ambata a takaice.

Na Farko, dole ne in mika godiya ta musamman ga wadanda suke halartar wuraren taruka a dandamali da masallatai a cikin wadannan kwanakin, kuma suke bayar da gudunmawa a harkoki na zamantakewa.

Da hakan ya hada da wasu bangarori na samar da kayayyaki, na gwamnati da wadanda ba  na  gwamnati ba, musamman ma abubuwan bukatar rayuwa na yau da kullum, musamman kuma yadda wasu mutane suka rika yin sadaukarwa ba tare sun cutar da kasuwarsu ba, har ma sukan raba kayayyaki kyauta ga mutane, mun gode wa Allah da samun irin wadannan mutane a cikinmu.

Na Biyu, Daya daga cikin hanyoyin aiki na makiya  shi ne ayyukan kafofin sadarwarsa, a cikin wadannan kwanakin musamman, suna kokarin ganin sun yi tasiri a kan daidaikun mutane da nufin rusa hadin kai da tsaro. Dole ne mu kula sosai, kada mu yi sakacin da hakan zai iya basu damar cimma mummunar manufarsu.

A kan wannan gabar ina son in jawo hankalin kafofin yada labarai na cikin gida na kasarmu, duk da mai yiwuwa su iya samun banbamcin mahanga ta siyasa da al’adu a tsakaninsu, amma su  guji nuna rauni da gazawa. Domin akwai yiwuwar makiya su yi amfani da hakan domin cimma burinsu.

Na Uku, daya daga cikin hanyoyin makiya shi ne yin amfani da rauni na tattalin arziki ko shugabanci. Shahidin jagoranmu Allah ya kara daukaka matsayinsa, a shekaru da dama ya mayar da hankali kan batun tattalin arziki wajen ayyana taken shekara.

A takaitacciyar mahangata, kyautata rayuwar mutane da bunkasa ababen more rayuwar jama’a da jin dadinsu, shi kansa mataki ne na tsaro, da ma kalubalantar matakan yakin tattalin arziki da makiya suka kaddamar.

Daga cikin abubuwan da na samu gamo-da-katar a kansu har da jin mahangar mutane daban-daban. Da hakan ya hada da haduwa da mutane da wadanda ba mu san juna ba, inda na kan zama fasinja abokin tafiya tare da ku a cikin motar haya ta tasi a kan titunan Tehran, ina jin ra’ayoyinku, wannan ya fi zama babbar hanyar jin ra’ayin jama’a. Abin da na iya fahimta dangane da kalamanku na yarda da mafi yawansu, wanda kuma akasari korafi ne game da batutuwa na tattalin arziki da gudanarwa.

Ta hanyar hakan na koyi abubuwa da yawa, kuma ina kara koyon wasu sabbin abubuwa. Daga cikin har da abubuwan da suka faru kafin da bayan 19 ga Ramadan a wuraren gangamin jama’a na koyi wasu abubuwa.

Ina fatan ba zan rasa wannan ni’imar ba. Daga abubuwan koyo da naji da kuma wadanda bibiya, akwai bukatar gagarumin aiki da himma tukuru da kuma  gogewa, da za su hada dukkanin banngaro, kuma godiya ta tabbata ga Allah, kusan dukkanin abubuwan da ake bukata akwai su, ba da jimawa ba ta hanyar aikin jami’ai masu himma tare da hadin gwiwa da sauran al’umma za a ga hakan a aikace da yardar Allah. A Wannan bangaren tare da yin koyi da babban jagora shahidi, taken wannan sabuwar shekarar shi ne “Tattalin Arziki Mai Juriya A Karkashin Hadin Kai Da Tsaron Al’ummar Kasa”

Na hudu kuma na karshe, abinda bawa Allah kaskantacce ya fada a bayani na farko dangane da ra’ayi da kuma siyasar tsarin gwamnati Iran dangane da dangantaka da kasashe makobta, al’amari ne mai muhimmanci da gaske.

Baza zamu iya raba al-amura da suka shafi makwobtaka, da wasu al-amura daga suka shafi hakan ba, kuma mafi muhimmanci daga cikinsu shi ne, riko da addinin musulunci a matsayin addini da ya hada mu, da kuma samuwar wurare masu tsarki da daukaka a cikin wasu kasashen, da samuwar Iraniyawa mazauna a cikin wadan nan kasashe ko masu aiki a cikinsu.

A wasu kasashen kuma akwai wasu wadanda muke hada harshe da al-adu da su, ko kuma abubuwa masu amfani, musamman wadanda muke fuskantar matsaloli da manya-manyan kasashen duniya saboda su. Ko wanne daga cikinsu ya isa ya karfafa dangantaka tsakanimmu da wadannan kasashe.

Daga ciki, muna ganin akwai kusanci mai yawa da makobtammu daga gabas, don na san cewa tun da dadewa, jagorammu shahidi, yana nuna matukar damuwarsa dangane da ambaliyar ruwa wanda ya tama lakume rayukan mutanen da dama a kasar Pakistan, inda ya bayyana damuwarsa a cikin wata khudubarsa ta jumma’a a lokacin.

Mu ma, tare da wasu dalilai daban daban, tunanimma kamar haka ne, kuma mun sha bayyana haka a tarurrukammu da dama. Don haka ina son in bayyana a nan, in kuma yi kira zuwa ga kasashe ‘yan uwammu, Afganistan da Pakistan, kan cewa saboda neman yardar Allah, kada mu raba kan musulmi, mu kuma samar da kekyawar hadin kai a tsakamimmu. Ni a bangare na, zan bada gudumawata da ya zama lazimi don tabbatar da hakan.

Har ila yau ina son tunatar da kasashen Turkiya da Omman wadanda muke da kekyawar dangantaka da su, kan cewa hare haren da aka kai kan wasu wurare a kasashensu, ba sojojin Jumhuriyar musulunci na Iran ne suka kai su ba, ba kuma mayaka masu gwagwarmaya a yankin ne suka kai here haren ba.

Wannan wani shiri ne na makiya yahudawa sahyoniyawa suka yi, don haddasa baraka tsakanin jumhuriyar musulunci ta Iran da makobtanta, kuma mai yuwa irin wannan ya sake faruwa a cikin wasu kasashen.

Sauran Magana wanda ya shafi wannan al-amarin mun ambacesu a baya. Ina fatan, tare da addu’o’in shugabammu, Allah ta’ala ya gaggauta bayyanarsa, da kuma taimakon Allah ta’ala, zamu shiga shekara mai al-barka, cike da nasarori, har’ila yau da budi mai yawa na duniya da lahira, ga al-ummar kasar Iran da kuma makobtanta, ga kuma sauran al-ummar musulmi, musamman ga masu gwagwarmaya a yankuna daban daban na kasashenmu. Sanna Allah ya sanya wannan shekarar, ba mai dadi ba ga makiyan musulmi da kuma bil’adama.

Allah yana cewa {Kuma muna son mu yi ni’ima ga wadanda aka kaskantantar da su a bayan kasa, mu kuma sanyasu shuwagabanni kuma Magadan kasa, kuma mu basu iko kuma mu nunawa fir’auna da hamana da kuma rundunoninsu, abinda suke jin tsaro}.

Allah madaukaki mai girma, ya fadi gaskiya da kuma manzonsa madaukaki kuma muna masu shaida a kan hakan. Amincin Allah madaukaki mai girma da rahamarsa da al-barkansa su tabbata a gareku.

 Sayyid Mujtaba Husaini Khamenei

20 Maris 2026

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted