Dakarun Kare Juyin Musulunci Na Iran Sun Kama Wasu Jiragen Ruwa 2 Na Masu Fasa kwaurin Mai A Tekun Fasha

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare  juya halin Musulunci na kasar iran IRGC sun sanar da kama jiragen ruwa guda biyu da ake fasakwaurin mai

Rahotanni sun bayyana cewa dakarun kare  juya halin Musulunci na kasar iran IRGC sun sanar da kama jiragen ruwa guda biyu da ake fasakwaurin mai da su a kusa da tsibin farisa, dake tekun fasha, kuma sun kama jiragen ne a yayin wani sintiri da suka gudanar kuma sun kama jiragen yana dauke da litar mai miliyan 1 da aka sata.

rahoton ya kara da cewa ana tsare da matukan jiragen ruwan guda 15 kuma an mika su zuwa ga bangaren sharia domin daukar matakin sharia da ya dace a kansu, kuma jiragen an nuna cewa sun dade suna aiki karkashin wata cbiyar masu fasakwabri na tsawon watanni.

Iran ta kara himma wajen dakile fasa –kwabrin albarkatun mai a tekun fasha , ana jigilar kayayyakin mai na mota ba bisa ka’ida ba zuwa kasashen larabawa dake yankin inda farashin mai zai iya ninka na cikin iran sau 20.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted