Iran ta yi gargadi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya game da barazanar da Amurka ta yi wa Tehran a bayyane.
Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya, Amir Saeed Iravani, ya ce kalaman barazana na Washington ba su takaita ga Iran kawai ba, yana mai tabbatar da cewa Amurka tana ci gaba da yin barazanar kai hari kan kasashe masu ‘yancin kai.
Ya bayyana barazanar da ake yi wa Tehran a matsayin bayyananne, yana mai nuna yadda Shugaban Amurka Donald Trump ya “yi barazana ga Iran a fili da kuma akai-akai da amfani da karfi da kuma tsoma baki na soja.”
Jakadan Iran ya bukaci kasashen duniya ya jaddada cewa dole ne Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da wadannan take hakki da Amurka ta aikata.
Sannan Iravani ya kawo misalai na “halayen da ba su dace ba na Washington” wadanda suka saba wa Yarjejeniyar, ciki har da rashin biyayya ga hukunce-hukuncen ICJ, da kame shugaban Venezuela, “barazanar da ke ci gaba, amfani da ƙarfi, da hare-haren soji a kan wasu ƙasashe masu ‘yanci,” da kuma “barazanar mamaye ko iko da yankunan ƙasashen waje.”
Wadannan kalaman sun biyo bayan jerin kalaman barazana da shugaban Amurka ya yi game da Iran, bayan zanga-zangar a Iran.