Jami’an diblomasiyya da jakadun kasar Iran a kasashen waje, da sauran ma’aikata a ma’aikatar harkokin wajen kasar Iran a cikin wani jawabin hadin guiwa sun jaddada goyon bayansu ga jagoran Juyin juya halin musulunci Imam Sayyid Aliyul Khaminaei, bayan barazanar da shugaban kasar Amurka Donal Trump yayi na cutar da shi.
Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto bayanin, wanda suka fito da shi a yau Talata, yana cewa, suna allawadi da kalaman Trump wadanda suka sabawa dokokin kasa da kasa kan wata kasa mai cikekken yanci. Sun kuma bayyana irin raunin da tsarin kasashe masu girman kai ke tafiya a duniya, wanda yake kalu bale ga masu gwagwarmaya a Iran da kuma yankin kudancin Asia.
Wadanda suka sanyawa bayanin hannu sun jaddada cewa wajibinsu ne su aiwatar da umurnin Jagoran dangane da harkokin diblomasiya a duk inda suka sami kansu a duniya. Kafin haka dai marigayi Imam Khomaini(q) ya sha nanata bukatar Jami’an gwamnatin kasar Iran su tsanantawa kasashe masu girman kai a duniya a duk wani wurin da ya dace su yi hakan.
Bayanin ya bukaci a hukunta Trump a kotun kasa da kasa, saboda ya aikata laifuka akalla ukku, wadanda suka hada da sabawa dokokin MDD, goyon bayan ayyukan ta’addanci a Iran da kuma barazana ga zaman lafiya a duniya.
Daga karshe bayanin ya bukaci dukkan musulmi, masu rajin kare hakkin bil’adama da kuma gwamnatoci masu yanzi a duniya su yi allawadai da Trump kan karya dokokin kasa da kasa da kuma halaye na barazana ga zaman lafiya a duniya.