Shugaban Venezuela Nicolas Maduro ya ce kalaman Shugaban Amurka Donald Trump game da “kwato” filaye da mai na Venezuela ya fallasa ainihin manufar Amurka, yayin da yake tabbatar da cewa Washington ba za ta “taɓa” mayar da ƙasar Latin Amurka ta zama “mallakarta ba.”
Da yake jawabi a wani gangami a Caracas ranar Laraba, Maduro ya ce kalaman Trump sun nuna cewa Amurka tana neman sauyi a tsarin mulki da iko a kan yankunan Venezuela da albarkatunta.
“Kawai dai wani makirci ne na nuna wariya da mulkin mallaka, kuma mun faɗi sau da yawa, kuma yanzu kowa yana ganin gaskiya ta bayyana,” in ji shi.
Maduro ya mayar da martani kai tsaye ga ikirarin Trump cewa Venezuela ta kwace man fetur, filaye, da sauran kadarorin Amurka, yana mai cewa ainihin manufar Washington ita ce ta kafa gwamnati a Venezuela wadda za ta mika ikon mallakar ƙasar.
Trump ya yi wannan tsokaci kwana ɗaya da ya gabata a dandalinsa na Truth Social, yana mai cewa tarin sojojin Amurka a kusa da Venezuela zai ƙaru har sai ƙasar ta dawo da “man fetur, ƙasa, da sauran kadarorin da suka sace daga gare mu a baya.”