Birtaniya Ta yi  Barazanar Yanke Gudunmawar Da Take Bawa Kotun Duniya

Babban mai shigar da kara a kuntun duniya mai hukumta manyan laifuka Karim Khan ya fadi cewa gwamnatin Birtaniya ta yi barazanar yanke tallafin da

Babban mai shigar da kara a kuntun duniya mai hukumta manyan laifuka Karim Khan ya fadi cewa gwamnatin Birtaniya ta yi barazanar yanke tallafin da take bawa kotun da kuma ficewa daga matsayin dake taimakawa wajen samun tallafi, idan kotun ta ci gaba da tafiya da sammacin da ta fitar na kama prime ministan israila banjamin Natanyahu

Khan yayi watsi da kiran da aka yi masa na ya jinkirta, yace babu wasu alamu dake nuna cewa isra’ila za ta bawa kotun ICC hadin kai ko kuma canza halayyarta a yankin Gaza, bayan da tel aviv ta fara musanta kisan kare dangi da ta yi a yankin gaza a watan oktoban shekara ta 2023

Sai dai fayel din da khan ya shigar ya fahimci cewa shi ne da kansa ya dage kan aikewa da martani mai shafuka 22 ga bukatar da isra’ila ta gabatar na yin watsi da sammacin bayan da ya sake duba abin da ya dauka a matsayin wani daftari ne da aka yi masa katsalandam,

Har ila yau ya tattara kwamitin kwararru kan harkokin sharia na kasa da kasa domin tantancewa ko kotun tana da hurumin yanke hukumcin wanda tel aviv ta ce ba ta da shi, da kuma duba shin ya kamata a gurfanar da Natanyahu da Gallant a gaban kuliya manta sabo.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted