Iran Ta soki Kasashe Masu Karfi Na Bawa Isra’ila Dama Ta Musamman Wajen Kai Hare-hare

Shugaban kasar Iran Masud pezeshkiyan a wajen taron zaman  lafiya na turkmanistan ya bayyana cewa siyasar kasashe masu karfin fada aji a yammacin Asiya ne

Shugaban kasar Iran Masud pezeshkiyan a wajen taron zaman  lafiya na turkmanistan ya bayyana cewa siyasar kasashe masu karfin fada aji a yammacin Asiya ne suka bawa isra’ila wata dama ta musamman  ta kai hare-hare gaba gadi, da hakan ya bata damar kai harin soji kan kasashen yankin ciki har da kasar iran ba tare da fuskantar wani sakamako ba.

Har ila yau shugaba peszeshkiyan da yake bayani a wajen taron zaman lafiya a garin Ashgabat na kasar Turkministan ya kara da cewa harin da Isra’ila ta kai wa iran a watan yuni da  ya kai ga shahadar mutane da dama da basu san hawa ba balle sauka ya samu kyakkawar tarba ne ma mai makon yin Allah wadai

Yace babu wani mataki na ladabtarwa da aka dauka ga wadda ta kai harin , ta ma samu cikakkiyar goyon bayan siyasa da soji ne daga kasahen masu ikirarin kare hakkin bil adama da kuma samar da zaman lafiya, matukar aka ci gaba da bada irin wannan dama ta musamman to babu wanda zai iya yin Magana kan zaman lafiya ko kuma wani umarni na kasa da kasa.

Daga karshe shugaba pezeshkiyan ya godewa Turkmenistan da ta dauki nauyin shirya wannan taro wanda ya zo dadai  da aka cika shekaru 30 da amincewa da zama yar baruwanmu a wannan kasa, kana kuma yayi kiran cewa suna goyon bayan  duk wani shiri na karfafa tunani kan zaman lafiya da tsaro da ci gaban dan adam da na dabi’a .

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted