Kremlin: Putin Ya Bayyana Wa Shugaba Maduro  Na Venezuela Goyon Bayansa

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Venezuela Nicholay Maduro ta wayar tarho inda ya bayyana masa cikakken

Shugaban kasar Rasha Vladmir Putin ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na kasar Venezuela Nicholay Maduro ta wayar tarho inda ya bayyana masa cikakken goyonbaya bisa barazanar da kasar take fuskanta daga Amurka.

Fadar mulkin kasar ta Rasha ta ce, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra’ayi akan hanyoyin bunkasa alaka a tsakaninsu.

Tun a baya, a yayin wani zama da kwamitin tsaro na MDD ya yi, wakilan kasashen Venezuela, Rasha da China, sun yi tir da yadda Amurka take jibge sojoji a yankin Caribbea, tare da bayyana hakan a matsayin barazana ga zaman lafiyar duniya.

Kasashen uku sun kuma bayyana wajabci kare hurumin kasar Venezuela da kuma kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gidanta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted