Ben Gafir Ya Sha Alwashin Rushe Kabarin Sheikh Izzuddin Alkassam

Ministan taron  Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ben Gafir ya sha alwashin rushe kabarin Sheikh Izzuddin al-Kassam dake kusa da birnin Haifa. Ben Gafir ya wallafa hotonsa

Ministan taron  Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ben Gafir ya sha alwashin rushe kabarin Sheikh Izzuddin al-Kassam dake kusa da birnin Haifa.

Ben Gafir ya wallafa hotonsa na tsokana a shafinsa n asada zumunta a kusa da makwancin shahararren malamin addinin mususulunci, tare da motar buldoza a kusa da shi, tana rusa wata hema da aka gina daura da kabarin, wacce mutane suke yin salla a cikinta da kuma yin addu’oi.

Sheikh Izzuddin al-Kassam  da reshen soja na Hamas ke dauke da sunansa, malamin addini ne wanda ya yaki Birtaniya da ‘yan sahayoniya a lokacin da suke share fagen gina haramtacciyar kasar Isra’ila. Ya yi shahada ne dan lokaci kadan gabanin shelanta kafuwar wannan haramtacciyar kasa a 1948. Makwancinsa a garin Naishar dake kusa da Haifa, a arewacin Falasdinu dake karkashin mamaya.

Ben Gafir ya ce; Wajibi ne mu rushe kabarin Sheikh Kassan dake garin Naishar, kuma a yau mun dauki hanyar yin hakan, saboda mu fara da rushe hemar dake kusa da kabarin.

A cikin watan Ogusta ta ne Ben Gafir ya fada a gaban majalisar Knesset ta ‘yan sahayoniya cewa; wajibi ne a rushe kabarin Kassam baki daya. Tun daga wancan lokacin ne aka  cire na’urar daukar hoto da take nuna abinda yake faruwa a wurin, sannan kuma aka kori mai tsaron wajen.

A gefe daya,kungiyar Hamas ta bayyana abinda Ben Gafir yake nufin aiwatarwa da cewa; kai wa kololuwar lalacewa ce ta ‘yan sahayoniya.

Jami’i a kungiyar Hamas Mahmud Murdawi ya ce, wannan matakin na Ben Gafir keta hurumin matattu ne da kuma wuraren addini,kuma laifin yaki ne.

Wannan dai ba shi ne karon farko ba da ‘yan sahayoniya suke kai wa wannan kabarin na Izzuddin Kassam hari, sai dai matakin da Ben Gafir yake son dauka a yanzu shi ne wuce gona da iri na koli akan wuraren masu tsarki na Falasdinawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted