Maduro: Amurka Ta Bude Sabon Salon Fashi Akan Doron Ruwa

Shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro wanda yake mayar da martani akan kwace jirgin ruwa na dakon man fetur da Amurka ta yi a kusa da

Shugaban kasar Venezuela Nicholas Maduro wanda yake mayar da martani akan kwace jirgin ruwa na dakon man fetur da Amurka ta yi a kusa da Venezuela ya ce; Abinda ya faru wani sabon salon fashi da makami ne akan doronĀ  ruwa da Amurkan ta bude.

A ranar Larabar da ta gabata ne dai sojojin Amurkan su ka kutsa cikin wani jirgin ruwa na dakon man fetur a tekun carriebia, su ka kwace iko da shi.

Wannan matakin da Amurkan ta dauka dai ya sa kasuwar man fetur ta duniya ta yi tangal-tangal,sannan kuma ya kara zaman man ja da doya dake tsakanin Amurkan da Venezuela.

A wata sanarwa da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Venezuela ta fitar ta yi tir da wannan halayyar Amurkan ta fashi da makami akan doron ruwa, kuma sata ce da kuma keta dokokin kasa da kasa.

A cikin watannin bayan nan dai Amurkan tana yawai kai wa kananan jiragen ruwa hari akan ruwan Carriebia tana mai riya cewa suna dauke da muggan kwayoyi ne daga Venezuela zuwa cikin kasarta.

Gwamnatin Venezuela dai ta sha karyata wannan zargin da Amurkan take yi ma ta.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted