Ansarallah: Dole Ne Kasar Yemen Ta Tsarin Musulunci Na Kaiwa Ga Daukaka

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa dole ne musulman kasar Yemen maza da mata sun bi tafarkin addinin

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen Sayyid Abdulmalik Badruddeen Huthi ya bayyana cewa dole ne musulman kasar Yemen maza da mata sun bi tafarkin addinin musulunci na kaiwa ga daukaka idan suna son daukaka.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran nakalto Al-Huthi yana fadar haka a jiya Laraba da yamma a lokacinda yake magana kan zagayowar ranar haihuwar Fatimah Azzahra diyar manzon Allah (s).

Malamin ya kara da cewa, Fatimah (a) abin koikoyo ne ga dukkan musulmi maza da mata a sanin Allah da halaye masu kyau don samun kusance ga Allah madaukakin sarki.

Al-Huthi ya kara da cewa a halin yanzu musulmi a ko ina suke a duniya suna fuskantar matsaloli, musamman musulman kasar Falasdinu wadanda HKI ta kashe dubban mutane daga cikinsu a cikin yan shekaru da suka gabata. Sun kashe mata da maza yara kanana hatta wadanda suke cikin iyayensu basu barsu ba.

Ya ce mafita ga musulmi itq ce koyi da iyalan gidan manzon Allah (s) musamman Fatima (a) don samun guzurin samun karfin fuskantar makiya a ko ina suke.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted