An cire Tony Blair daga jerin wadanda zasu jagoranci Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta yi maraba da bayannan cewa an cire sunantsohon firaministan Burtaniya Tony Blair daga wadanda ake tunanin zasu jagoranci Gaza

Kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas, ta yi maraba da bayannan cewa an cire sunantsohon firaministan Burtaniya Tony Blair daga wadanda ake tunanin zasu jagoranci Gaza a shirin zaman lafiya na shugaban Amurka Donald Trump a Gaza.

Jaridar Financial Times ta ruwaito a ranar Litinin cewa kasashen Larabawa da na Musulmi ne suka nuna adawa da shigar da M.Blair cikin “hukumar rikon kwarya” da Trump ya bayyana a matsayin wani bangare na shirinsa na zaman lafiya a Gaza.

Tony Blair ya sha suka a faɗin duniyar Musulmi saboda rawar da ya taka a mamayar da Amurka ta jagoranta a Iraki a shekarar 2003, wanda daga baya aka gano cewa kawai zarge-zargen karya ne.

Wani Jami’in Hamas, Taher al-Nunu, ya ce rahotannin yiwuwar cire Blair ya yi daidai da kiran da kungiyar ta yi ga masu shiga tsakani don hana shi shiga kowace hukuma da ke da alaka da Gaza.

A daya bangaren kuma Al-Nunu ya sake nanata cewa ƙungiyar ta kasance “a shirye don tsagaita wuta na dogon lokaci” muddin gwamnatin Isra’ila ta amince da dukkan sharuddan tsagaita wuta, wani abu da Tel Aviv ta kauce masa zuwa yanzu ta hanyar karya yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma a farkon watan Oktoba.

Jami’in na Hamas ya kuma jaddada cewa duk wani shiri da ya shafi rundunar ƙasa da ƙasa da aka ɗora wa alhakin kwance damarar yaƙi da ƙungiyoyin gwagwarmaya da ƙarfi, “an yi watsi da shi kuma ba a taɓa tattauna shi ba.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted