A wani rahoton da jaridar Jerussalam Post” ta buga ta ambaci cewa; Tun bayan farmakin 7 ga watan Oktoba 2023, ana kara samun matalauta da talauci.
Rahoton ya yi nuni da cewa karuwar talaucin yana da alaka ne da yadda farmakin 7 ga watan Oktoba ya yi tasiri a cikin tattalin arziki “Isra’ila”.
Haka nan kuma rahoton ya ce, da akwai dubban iyalai yahudawa wadanda gabanin yaki, suke rayuwa cikin yanayi mai kyau ta fuskar tattalin arziki, yanzu sun zama matalauta. A dalilin haka cibiyar da ta shirya rahoton ta “ Latit” tana yin gargadi akan cewa; za a iya samun ci gaba da yaduwar talaucin, domin iyalai da dama suna gogoriyon yadda za su iya biyan bukatar yau da kullum, duk da cewa suna da cikakken aiki.
Ita dai kungiyar “Latit” ta ‘yan sahayoniya ce wacce aka kafa a 1996 domin fada da talauci da kuma rashin abinci.
Haka nan kuma rahoton ya bayyana cewa; Adadin iyalan da suke fama da talauci a cikin ‘yan sahayoniyar sun kai 867,000, saboda ba su da lamunin abinci. Adadin daidaikun wadannan iyalan sun kai miliyan 2.8, daga cikinsu da akwai kananan yara miliyan 1.18.
Haka nan kuma wani sashen na rahoton ya ce, talaucin yana karuwa ne da kaso 27-29%.
Da dama daga cikin iyalan ‘yan sahayoniyar suna rayuwa ne ta hanyar samun taimako da tallafi na abinci,domin suna amfani da kudaden da suke samu na aikin yi, domin biyan kudaden wuta da sayen magunguna.
Kaso 40% na tsofaffi suna fama da matsalar tabarbarewar rashin lafiya, da ya faro tun daga farkon yaki.