AU Ta yi Tir Da Harin RSF  A Makarantar Kananan Yara Da Ya Kashe Mutane 80

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi tir da harin RSF kan wata makarantar kananan yara a kudancin Sudan da ya kashe dimbin fararen hula

Kungiyar Tarayyar Afrika ta AU ta yi tir da harin RSF kan wata makarantar kananan yara a kudancin Sudan da ya kashe dimbin fararen hula tare da jikkata da dama, mafi muni a baya-bayan nan da kungiyar ta kai a kokarin da ta ke yi na ci gaba da kwatar yankuna a sassan Kasar.

Akalla mutane 80 mafiyawancinsu  kananan yara ne suka mutu a  harin da mayakan RSF suka kai bayan da suka jefa bama-bamai kan wata makarantar kananan yara da ke garin Kalogi na yankin Kordafan a kudancin Sudan.

Rahotanni sun ce hare-hare 3 da RSF ta kai a yankin lokaci guda, inda a farko mayakan suka jefa bama-bamai a makarantar kananan yara gabanin kai hari wani asibiti kana daga bisani suka sake jefa wani bom kan wadanda ke kokarin kai dauki  a makarantar kananan yaran.

Shgaban gwamnatin garin na Kalogi da harin ya faru Essam al-Din al-Sayed ya ce yanzu haka babu sadarwa a garin sai dai ta hanyar amfani da Starlink, kuma tsagin RSF da Abdelaziz al-Hilu ke jagoranta ne ke kaddamar da hare-haren kan mata da kananan yara a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted