Iran Da Kasashen Afrika Sun Daura Dammarar Karfafa Alakar Kimiyya Tsakaninsu

A cikin wani taron hadin guiwa da aka yi takanin iran da sauran jakadun kasashen afrika guda 19 da sauran jami’an kasar iran, sun jadadda

A cikin wani taron hadin guiwa da aka yi takanin iran da sauran jakadun kasashen afrika guda 19 da sauran jami’an kasar iran, sun jadadda game da muhimmancin yin aiki tare a bangaren ilimi, bincike da kuma kiwon lafiya, da kuma yadda zaa kara karfafa alaka tsakanin Iran da kuma nahiyar Afrika.

Taron ya nuna irin ci gaban da aka samu daga yin aiki tare na lokaci bayan lokaci zuwa hadin guiwa da iran ta hanyar ilimi da kiwon lafiya, da kuma yin aiki tare a bangaren kimiya da nahiyar Afrika, wannan abin da aka kirkiro zai tunkari barazanar da ake fuskanta na yaduwar cututtuka, karancin magani da kuma ayyukan lafiya a yankunan karkara a Afrika.

Jami’ar llimin likitanci ta birnin Tehran ta ce ba wai kawai ta dauki kanta a matsayin jigo a bangaren ilimi ba ne, har ma a matsayin wata madogara wajen ayyukan kiwon lafiya na kasa, wanda zai iya jurewa takunkumi, ta hanyar bude dakunan gwaje-gwaje, cibiyoyin bincike da kuma shirye shiryen ilimi ga abokan hulda a Afrika,

Iran tana son gina gada mai tsawo ta yin hadin guiwar kimiyya da nahiyar Afrika.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted