An Kashe Shugaban ‘Yan Dabar Gaza “Abu Shabab” Da Isra’ila Ke Goyon Baya

Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ce an kashe shugaban kungiyar ‘yan daba na Gaza Yasir Abu Shaba,ba tare da an tantance wanda ya yi hakan

Kafafen watsa labarun “Isra’ila” sun ce an kashe shugaban kungiyar ‘yan daba na Gaza Yasir Abu Shaba,ba tare da an tantance wanda ya yi hakan ba.

Kafafen watsa labarun “Isra’ilan”sun ce; Kashe Abu Shabab wani mummunan labari ne ga Isra’ila.”

Tashar talabijin 12 ta ambato wani jami’in tsaro yana cewa; Abu Shabab ya cika ne a asibiti saboda raunin da ya samu daga harbin da aka yi masa a wani sabani na cikin  gidan.”

Sai dai wata majiyar ta ce, da akwai yiyuwar kungiyar Hamas ce ta kashe shi, bayan da ta tattara bayanai akansa daga makusantansa.

 An fara jin duriyar Abu Shabab ne a ranar 30 ga watan Mayu 2025 bayan da kungiyar Hamas ta watsa wani faifen bidiyo akan bayanan da ta tattara dangane da rundunar da ake kira ta” Mus’ta’aribin” ko kuma mayakan ‘yan sahayoniya larabawa da yadda suke gudanar da ayyukansu a  gabashin garin Rafah a kudancin Gaza.

Abu Shabab da kungiyarsa ta ‘yan daba mai suna “Tanzim al-quwwatuls-sha’abiyyha” sun rika barna a tsawon lokacin yakin Gaza, ta hanyar sace kayan agaji da taimakawa sojojin Sahayoniya suna cutar da ‘yan gwgawarmaya da kashe su.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted