Hamas Za ta Mikawa Isra’ila Samfurin  Da Aka Samu A Karkashin Burabutsai A Gaza

Rahotanni sun bayyana cwa kungiyar Hamas tace za ta mikawa isra’ila sabon samfurin jikin dan Adama da ta samu a arewacin gaza, bayan da isra’ila

Rahotanni sun bayyana cwa kungiyar Hamas tace za ta mikawa isra’ila sabon samfurin jikin dan Adama da ta samu a arewacin gaza, bayan da isra’ila ta yi ikirarin cewa gawarwakin da kungiyar gwagwarmaya ta basu ba su daga cikin gawarwaki guda biyu da su ke rike da su da har yanzu ba’a dawo da su ba,

Kungiyar ta hamas ta bayyana cewa dakarunta da hadin guiwa dakarun kungiyar jihadil Islami suna aiki tare kuma sun gano wani burbushin jikin dan adam da suke ganin yana da alaka da bayahuden da suka kama ne beneath a karkashin burabutsai a yankin beit lahia,

Kuma za ta mika samfurin zuwa isra’la ta hannun babban kwamitin kungiyar bada agaji ta red cross ta ksa da kasa domin gudanar da bincike a kai,

Bisa yarjejeniyar dakatar da bude wuta da aka cimma a watan oktoba kungiyar gwagwarmaya ta hamas za ta mika yahudawan da take tsare da su guda 48da suka hada da guda 20 da har yanzu suke raye.

Masharhanta sun yi amanna cewa batun shirin dakatar da bude wuta da trump ya bullo da shi zai bawa kasashen duniya damar kawar da kansu game da laifukan yaki da HKI ta tafka, kuma zai bawa kasashen turai mafakar siyasa a daidai lokacin da yanayin da ake ciki yake kara tazzara.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted