Kungiyoyin farar hula na kasar Chile za su bude yin kira da a kori Haramtacciyar Kasar Isra’ila daga Majalisar Dinkin Duniya saboda yadda take ci gaba da keta dokokin kasa da kasa.
A yau ranar 26 ne ga watan Nuwamba ne kungiyoyin za su bude wannan yin kiran a birnin ” Santiago”. Tun da fari, kungiyoyin sun bude shafi a hanyar sadarwa ta “Internet” domin bayar da dama ga mutane su nuna goyon bayansu ga Shirin korar HKI daga Babbar cibiyar ta kasa da kasa.
Kafar watsa labaru ta “Quds Press” ta amabaci cewa; Wasikar da kungiyoyin fararen hular za su aike wa babban sakataren MDD Antonio Gutrres tana kunshe da sanya hannu na mutane 57,000,amma ana son wannan adadin ya kai 100,000.
Wadanda su ka shirya wannan kamfen din sun bayyana jin dadinsu akan yadda al’umma take karba kiran nasu cikin gaggawa .
Haka nan kuma sun bayyana cewa, kamfen din nasu an gina shi ne akan doka ta 6 ta dokokin MDD dake cewa duk wata kasa memba wacce ta keta doka za a iya korarta.
Har ila yau kungiyoyin fararen hular sun kuma ce, za su yi amfani da hanyoyin diplomasiyya da diplomasiyya domin ganin manufarsu ta korar “Isra’ila” daga MDD ta tabbata. Wani lauya kuma tsohon jakadan kasar Chile Nelson Haddad ya bayyana cewa: Isra’ila ta zama kasar da ake kyama, bisa dokokin kasa da kasa, domin ba ta aiki da dokokin MDD balle kuwa dokokin jin kai na duniya.”