Afirka Ta Kudu: Rashin Halartar Amurka Taron G-20 Ba Zai Yi Wani Tasiri Ba

Shugaban bangaren sandarwa da bayanai na gwamnatin Afirka Ta Kudu, William Bawli ya ce; rashin zuwan Amurka taron kungiyar G 20 da ake yi a

Shugaban bangaren sandarwa da bayanai na gwamnatin Afirka Ta Kudu, William Bawli ya ce; rashin zuwan Amurka taron kungiyar G 20 da ake yi a kasar babu wani tasiri da zai yi.

William ya kuma ce, idan Amurkan ta sauya ra’ayinta za ta iya zuwa kuma ana maraba da ita.

Shugaban bangaren sadarwar na gwamnatin Afirka Ta Kudu, ya fadawa kamfanin dillancin labarun “Sputnik” na Rasha cewa; Tun daga lokacin da kasar ta Afirka Ta Kudu ta karbi jagoracin kungiyar ta G 20,a 2024 an yi taruka har sai 130 a matakan ministoci da kuma kasa da haka,kuma Amurkan ta rika halartar wasu daga cikin wadannan tarukan.

Amurka dai ta yanke shawarar kin halartar taron na kungiyar G 20 da aka bude a birnin Johanusbourg na kasar Afirka Ta kuda wanda kuma zai ci gaba har zuwa gobe.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted