Kakakin majalisar dokokin kasar Iran mohammad Bhakir Qalibaf ya bayyana cewa makiya JMI sun sawya salon yakaar kasar kamar yadda suka saba, a halin yanzu sun fibada karfi kan takurawa tattalin arziki da rikita al-adu da kuma zamantakewa tsakaninmutanen kasar.
Kamfanin dillancin labaran IP nakasar Iran ya nakalto Qalibaf yana fadar haka a jiya jumm’a a wani taro na mayakan sa kai a nan birnin Tehran a jiya Jumma’a ya kuma kara da cewa, da wannan dalilin ne gwamnatin kasar ta ke karfafa kira ga mutanen kasar su kiyaye hadin kan da suke da shi, su kara dankon zumunci da ke tsakanin kabilu da bangarorin kasar don hana makiya cimma manufofinsu a wannan yakin da ke yi da kasar.
Yayi kira ga gwamnatin kasar ta kara karfi wajen kyautata rayuwar mutanen kasar don hana makiya duk wata dama ta inda zasu shiga a bata zamantakewa tsakaninmutanen kasar Iran.