Shugaban majalisar dokokin kasar Labanon Nabih Berri yayi kira da a gudanar da taron gaggawa na kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya domin tattaunawa kan ci gaba da keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta da Israi’la ke yi kan kasar Labanon, wanda ya kashe mutane 14 , kuma ya jaddada game da muhimmancin shigar da kara a hukumance ga majalisar dinkin duniya.
Wannan bukata ta zo ne adaidai lokacin da sojojin Isra’ila suke kai hare hare kan fararen hula dake jawo asarar rayuka, kuma yake jawo fargaba game da ci gaba da hara-haren israila na keta yarjejeniyar dakatar da bude wuta mai lamba 1701, Isra’ila ta kai hare hare a lokuta daban daban a kudancin labanon kuma yayi sanadiyar mutuwar mutane da dama.
Nabih Birri ya kara da cewa Isra’ila taci gaba da kai hare hare kan fararen hula, yara da kuma dalibai wanda na baya bayan ne shi ne ta kai a garin Al- Tira,
Ana ta bangaren kungiyar hizbullah ta yi tir da harin kisan kare dangi da sojojin Isra’ila ke yi a kudancin labanon ,kuma ta bayyana shi a matsayin mummunan aiki dake kara yawan tarihin laifukan yaki kan alummar falasdinu da ma labanon dama sauran mutanen yankin da Isra’ila ke yi.