Lebanon: Mutane 2 Sun Jikkata Sanadiyyar Harin “Isra’ila” A Garin Bint-Jubail

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Asabar ne jiragen yakin HKI su ka kai hari a garin Bint Jubail

Tashar talabijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; Da safiyar yau Asabar ne jiragen yakin HKI su ka kai hari a garin Bint Jubail dake kudancin kasar.

Harin na jiragen Sahayoniya dai ya kasance ne a kusa da aibitin Salah-Gandur da hakan ya yi sanadin jikkatar wasu mutane biyu.

Wasu yankunan da jiragen sama marasa matuki na Haramtacciyar Kasar Isra’ila su ka kai wa hare-hare sun hada Jan’am dake gababsin Shaba’a, da Rashiyal-Wadi. Sai kuma kusa da garin Balida.

A jiya Juma’a ma dai ‘yan sahayoniyar sun kai wasu hare-haren a kudancin Lebanon da su ka hada da Jabalus-Salihin,da Sahalul-Kiyam, sai Tallatul-Hamamis.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted