Araqchi: Haramtacciyar Kasar Isra’ila Ita Ce Babbar Tushen Bullar Tashe-Tashen Hankula A Yankin

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas

Ministan harkokin wajen kasar Iran ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin

Ministan Harkokin Wajen Iran Abbas Araqchi, yayin da yake magana kan kalaman Fira Ministan gwamnatin ‘yan sahayoniyya ya ce: “Gwamnatin Yahudawan Sahayoniyya ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.”

A shafinsa na Twitter, Araqchi ya rubuta cewa: Wannan abin da ake kira “tushen tsaro a Gabas ta Tsakiya” ana nemansa ne saboda kisan kare dangi da laifukan yaƙi. Yana sanya tsarin wariyar al’umma ga Falasdinawa miliyan 7.5, ya jefa bama-bamai a ƙasashe bakwai a bara, kuma ya mamaye yankunan Falasdinawa, Lebanon, da Siriya.

Ya ƙara da cewa: “Gwamnatin ‘yan sahayoniyya tan zama ita ce babbar tushen rashin zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.”

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted