Zanga zanga Ta Barke A Birmingham Ta Nuna Kin Jinin Isra’ila .

Rahotanni su bayyan cewa zanga-zanga ta barke a wajen filin wasan kwallon kafa a Birmingham kafin fara gasar kwallon kafa tsakanin isra’ils maccabe tel aviv

Rahotanni su bayyan cewa zanga-zanga ta barke a wajen filin wasan kwallon kafa a Birmingham kafin fara gasar kwallon kafa tsakanin isra’ils maccabe tel aviv da kuma England Ason villa inda suke yi ta rera taken nuna damuwa da halin da yankin Gaza ke ciki da kuma yin kira ga hukumar fifa da ta kori Isra’ila daga cikintta,

Wannan yana nuna irin yadda kin jinin Isra’la ya yadu a duniya saboda irin kisan gillan da take yi wa alummar gaza, inda lamarin ya shafi hatta a harkokin wasanni da sauran rayuwar alumma a kasashen turai .

Rahotano da jaridar the independent ta nakalto ya nuna cewa magoya bayan falasdinawa sun lika hotuna a fadin birnin dake yin kira ga hukumar fifa da ta dakatar da wasan kuma sun kewaye filin wasan da tutocin falasdinu , sai dai magoyan bayan kungiyar kwallon kafa ta Maccabi yan tsiraru sun tsaya cirko-cirko a wajen.

Gwamnatin birtaniya ta aike da jami’an yan sanda sama da 700 a wajen domin tabbatar da tsaro, masu rajin kare hakkin dana dam suna ta kiraye –kirayen korar isra’ila daga fifa kuma sun bayyana wasan a masatayin abin kunya a daidai lokacin da isra’ila ke kisan gilla a gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted