Kamfanin dillanacin labarun Faransa ya ambato wata majiyar shari’a tana cewa; ‘yan jaridar da aka kama su ne; Ibro Shu’aibu na gidan talbijin din Sarauniya, sai Yusuf Sariba na wani Shafin watsa labaru na Niger Ecoh da kuma Umaru Kani na jaridar “Errison.”
Dukkanin ‘yan jaridar uku an kai su kurkukun Kolo wanda yake da nisan kilo mita 50 daga babban birnin kasar Yamai. A ranar Asabar din da ta gabata ne dai aka kama wadannan ‘yan jaridar da kuma wasu abokan aikinsu.
Ana tuhumar ‘yan jaridar da fallasa bayanan gwamnati da shi ne bukatar samarwa da gwamnatin taimakon kudi daga ‘yan kasa.
Bayan watsa labarin da aka zargi tashar talabijin din Sarauniya da yi, labarin ya watsu a cikin kafafen sadarwa na al’umma, kuma magoya bayan hambararren shugaban kasar Muhammad Bazum, sun rika amfani da shi domin yin batunci ga gwamnati.
A watan Satumba na wannan shekarar ma an daure wani dan jarida mai suna Hassan Zada na tsawon watanni 30, bisa samunsa da laifin cin zarafin shugaban kasa.
Kungiyoyin kare hakkin bil’adama da su ka hada da “Amnesty International” suna cewa ana samun Karin take hakkoki a cikin kasar ta Nijar.