Ministan harkokin wajen Iran ya jaddada cewa: Isra’ila ba za ta kai hari kan Iran ba sai da goyon bayan Amurka
Ministan harkokin wajen Iran Seyyed Abbas Araqchi ya bayyana cewa: Gwamnatin ‘yan sahayoniyya ba za ta kaddamar da yaki kan Jamhuriyar Musulunci ba tare da samun wata kariya daga Amurka ba. Ya kara da cewa, Iran ta gudanar da yakin kwanaki goma sha biyu da wannan gwamnati mai wuce gona da iri, kuma ta hana ta ci gaba da mummunar manufarta ta mamaya a yankin.
A wata hira da ya yi da gidan talabijin na Al- Jazeera, Araqchi ya yi nuni da cewa: Gwamnatin masu wuce gona da iri ta yi kokarin fadada yakin zuwa yankin ta hanyar kai hari kan cibiyoyin man fetur na Iran, amma Iran ta yi nasarar shawo kan yakin kuma ta hana aukuwan hakan.”
Yayin da yake fayyace shirye-shiryen Jamhuriyar Musulunci ta Iran na tattaunawa don kawar da damuwar da ake da ita game da shirin makamashin nukiliyarta na zaman lafiya, Ministan Harkokin Wajen ya jaddada cewa: “Sun shirya wa duk wani abu da zai faru kuma suna tsammanin duk wani hali mai tsauri daga ‘yan sahayoniyya.” Ya bayyana cewa Iran ta samu kwarewa mai yawa daga yakin da ta yi kwanan nan kuma ta samu damar gwada makamai masu linzaminta a wannan yaĆ™i na gaske.